Dakarun sojan Najeriya sun ce kashe ƴan bindiga uku a Jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ta ce sun kashe ƴan bindigar ne waɗanda suka kai wa ƴan sanda hari ranar Alhamis a wani shingen binciken jami’an tsaro kan babbar hanyar Okija-Onitsha a ranar Alhamis.
Ya ce ɓangaren dakarun rundunar Golden Dawn da aka tura Enugu sun murƙushe ƴan bindigar a musayar wuta, wanda ya tursasa masu tserewa.
“Yan bindiga uku aka kashe, waɗanda ke cikin mota biyu ƙirar Hilux da Hummer, yayin da wasu suka tsere da harbin bindiga a jikin su.