Rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar hallaka gawurtaccen dan ta’addan nan Dogo Umaru wanda yake gaba gaba a tawagar Bello Turji tare da kashe wasu ‘yan ta’addar guda 40.
An rawaito cewa harin saman da aka kai musu a maboyarsu ta biyo bayan umarnin da rundunar tasu ta basu bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa Dogo Umaru da mukarrabansa sune suke shirya muna nan hare hare a garin Magama dake karamar hukumar Jibiya ta jihar, inda daya daga cikin harin da suka kai yayi sanadin mutuwar baturen ‘yansandan garin na Magama tare da raunata wani jami’in soja.
Rahotanni sun bayyana cewa Dogo Umaru tare da mabiyansa suna aiwatar da haramtattun aika aikecen nasu ne daga wata makarantar firamare dake yankin wadda ake ake kira Tsamben Dantambara, wadda tuni aka rushe ta bayan luguden wuta da rundunar sojin saman tayi a wajen.
Wasu majiyoyi a garin na tsamben babare sun bayyana cewa akalla ‘yan ta’addar 42 ne suka rasa rayukansu a harin da rundunar sojin saman kasar nan suka kai musu cikinsu har da Dogo Umaru