Shugabannin duniya na yin tir da harin da aka kai wa firaministan Slovakia

Daga ketare; Shugabannin duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da harin da aka kai kan firaministan Slovakia.
Shugaba Biden ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan abin tashin hankali.
Shugaba Putin ya bayyana Mista Fico a matsayin mutum mai jajircewa kuma mai kaifin tunani.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa wannan hari ne kan dimokuradiyya, yayin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce bai kamata irin wadannan hare-hare su zama ruwan dare ba.

Leave a Reply