Wasu daga cikin shugabannin hukumar gudanarwar Barcelona sun bukaci shugaban kungiyar Joan Laporta da ya kori kociyanta Ronald Koeman bayan da Bayern Munich ta lallasa su 3-0 ranar Talata a gida a gasar zakarun Turai.
Sannan ya kasa tabuka komai tu bayan da kungiyar ta Barcelona ta dauke shi aiki a matsayin kocin kungiyar a shekara ta 2019.