Shugaban kasa Bola Tunubu ya nada sabbabin mutanen da zasu taimaka wajen bunkasa harkar ilimin jami’o’in Najeriya

Shugaban kasa Bola ahmad Tunubu ya nada tsohon shugaban sakataren gwamnatin tarayya Alhj Yayale Ahmad da kuma tsohon gwamnan jahar Bauchi Alhj Isa Yuguda, da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Prof Attahiru jega da karin wasu sabbabin mutanen da zasu taimaka wajen bunkasa harkar ilimin jami’o’i ta kasa.
Sabbin mambobin akwai Alhj Muhammada Abacha dan gidan marigayi Sani Abacha da sanata Udoma Udo Udoma, PROF Munzali Jibril, Chief Wole Olanipekun SAN Sen Joy Emordi da Prof Julius Okojie, da wasu daga cikin su.
A ciki sun hada da mutum 50 daga jami’oi 37 daga makarantun kimiyya da fasaha da kuma 24 daga kwalejin koyo da koyarwa .
Daga cikin wayanda aka zaba akwai mataimakin shugaban jami’oi da kuma membobi daga gwamnati da mutane 111 daga cikin manyan jami’oin tarayyan, da makarantun kimiyya da fasaha da kwalegin ilimi ta koyo da koyarwa.

Leave a Reply