Shugaban jam’iyyar APC ta Kasa Adams Oshiomole, ya yi watsi da matakin da jam’iyyar PDP tace zata dauka……

Shugaban jam’iyyar APC ta Kasa Adams Oshiomole, ya yi watsi da matakin da jam’iyyar PDP tace zata dauka kan ‘ya’yanta; bisa yadda suka gudanar da zaben shugabannin Majalisa ta 9.

Oshiomole, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar tawagar gwaman jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da suka ziyarci shi a Abuja, domin yin godiya ga matakin da jam’iyyar ta dauka na zaben Hon. Alhassan Ado Doguwa, a matsayin jagoran majalisar .

Gamnan , wanda ya  samu wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da daukacin mambobin majalisar wakilai daga nan jihar Kano, ya yabawa jam’iyyar APC kan  namijin kokarin da tayi na zaben Hon. Doguwa.

Daga cikin tawagar akwai dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Ungogo da Minjibir Hon. Sani Ma’aruf Maiwake da takwaransa na Bichi .

PDP dai na zargin cewa mambobinta sun yi ba daidai ba, a lokacin da aka gudanar da zaben shugabannin majalisa ta 9, inda jam’iyyar ta PDP ta nada tsohon shugaban Majalisar Dattawa Adolphos Wabara, a matsayin shugaban kwamitin binciken.