Shugaban hukumar EFCC yace manufar fasalta Naira shine hana wawure dukiyar al ummar Najeriya.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC Abdulrasheed Bawa, yace matakin da aka dauka na sake fasalta kudin Najeriya anyi shi ne da nufin tilasta dawo da kudaden al’ummar kasar nan da aka wawure.

Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana cewa shawarar da aka yanke ta fasalta kudin babu siyasa a ciki.

Yace shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rigada ya amince da shawarar da babban bankin Najeriya CBN ya bayar na sauya fasalin kudin kasar nan.

Acewar shugaban na EFFC idan aka sauya fasalin naira ana saran dalar Amurka zata sauko daga 880 zuwa 680 har zuwa 200 a Najeriya.

Leave a Reply