Shugaban Belarus ya ce zai sake bai wa Rasha damar kai hari Ukraine

Shugaban kasar Belarus, Alexander Lukashenko, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya bar Rasha ta yi amfani da ƙasarsa wajen ƙaddamar da sababbin hare-hare a kan Ukraine.

Shugaba Putin ya tura dakarunsa ƙasar ta Belarus a bara a farkon mamayar da ya yi wa Ukaraine.

Mista Lukashenko ya ce zai iya sake bayar da wannan dama kamar yadda ya yi a baya.

Shugabana ya ce a shirye yake ya yi fada tare da sojojin Rasha a yankin da ke ƙarƙashin ikon Belarus.

Amma ya ce zan yi hakan ne idan wani sojan Ukraine ya shiga yankin ƙasarsa da bindiga domin ya kashe alummarta.

Ya kuma gayyaci Shugaba Biden da ya je Minsk babban birnin ƙasar Belarus domin su gana da Shugaba Putin a kan yadda za a sasanta ɓangarorin biyu

Leave a Reply