Shugaban Amurka ya yi watsi da buƙatar kama Firaministan Isra’ila

Shugaba Biden ya sake jaddada matsayar sa ta kare Isra’ila, sa’oi kaɗan bayan mai gabatar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya ce ya nemi a bashi izinin kama Benjamin Netanyahu da kuma ministan tsaron sa, a bisa zargin aikata mummunan manyan lafuka a Gaza.

Da yake tsokaci a kan shari’ar da aka yi mataki-mataki a kotun ta duniya, Mr Biden ya haƙiƙance cewa dakarun Isra’ila ba su aikata kisan gilla a Gaza ba.

Manyan sanatocin Amurka daga democrat da kuma republican sun Allah wadai da matsayar mai gabatar da ƙarar na kotun duniya,

Tun da farko dai, Firaiministan Isra’ila Banjamin Netanyahu ya yi Allah-wadai da bukatar mai gabatar da kara na Kotun Duniya ta neman a kama shi da wasu shugabannin Hamas bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza.

Leave a Reply