Shugaba Tinubu Ya Nemi Rancen Dala Miliyan 500 Daga Bakin Duniya


ASALIN HOTON,BOLA TINUBU/FACEBOOK

Gwamnatin tarayya na neman rancen dala miliyan 500 daga bankin duniya domin inganta hanyoyin karkara da kuma bunƙasa noma.

Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa nn zayyana wannan yunƙurin ne a cikin daftarin ƙarshe na tsarin sauyawa mutane matsugunu da bunƙasa harkar noma (RAAMP-SU), wanda Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta najeriya ke gudanarwa.

Bashin kuɗin na nufin magance matsalolin da mazauna yankunan karkara miliyan 92 ke fuskanta waɗanda a halin yanzu ba su da hanyoyi masu kyau.

Takardar manufofin ta nuna manyan tituna a Najeriya, waɗanda suka haɗa da kusan kilomita 194,000.

Waɗannan hanyoyin sun ƙunshi na gwamnatin tarayya mai nisan kilomita 34,000, da titin jahohi 30,000, da titin ƙananan hukumomi kilomita 130,000 da kuma bunkasa kasuwancin noma.

Tsarin yana mai da hankali ne kan haɓaka hanyoyin shiga karkara da inganta batun sauyin yanayi da kuma kasuwancin kayan gona da noman kansa.

BBCHAUSA

Leave a Reply