Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Matsalolin Tattalin Arziki Da Tsaro

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar a zauren majalisar dokoki da ke birnin tarayya Abuja.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Alhamis ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, da babban sufeton ‘yan sanda Olukayode Egbetokun.

Taron dai ya biyo bayan taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa wanda ta saba gudanarwa a kowane wata wanda mataimakin shugaban kasa Shettima ya jagoranta.

Bayan kokawa da al’ummar Najeriya suke ci gaba da yi kan tabarbarewar tsaro da tattalin arziki, shugaban kasar ya umarci ma’aikatar noma da samar da abinci ta fitar da kimanin tan dubu arba’in da biyu na masara da gero da sauran kayayyakin masarufi a wani yunkuri na magance hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ta yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin daidaita al’amura, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da ribar da kowane dan kasa zai ci moriyar sa nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply