Shugaba Donal Trump na Amurka, yayi amai ya lashe akan harba makami mai linzami ga Iran

Kafofin yada labaran Kasar Amurka sun sanar da cewa Shugaba Donal Trump na Amurka, amince da harba makamai masu linzami zuwa Kasar Iran; sannan daga bisani yayi amai ya lashe.

Jaridar New York Times, ta fitar da sanarwar cewa Manyan jami’an fadar “white house” sun ce harin wani mataki ne na farwa Kasar Iran kan shirinta na mallakar makamin nuclear, wanda hakan barazana ce ga bil’adama.
Wannan ya faru ne bayan kasar Iran ta kakkabo jirgin Amurka mara matuki daga sararin samaniyarta.

Ana dai ta zaman zullumi a tsakanin kasashen biyu, inda Amurka ta zargi Iran da kai hari kan jirgin Kasar Japan, a daidai lokacin da shugaban Kasar Japan Shinzo Abe ka ganawa da Ayatullah Khamne;I a Tehran. Sannan hukumomin Iran sun sanar da cigaba da ayyukansu na sarrafa makamashin Nuclear.