Shugaba Buhari zai tafi taron Tarayyar Afirka a Ethiopia

Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 36, a yau Alhamis.

A wata sanarwa da kakakin shugaban, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya ce, a yayin da yake birnin na Addis Ababa, Buharin zai halarci wasu manyan taruka uku, a kan tsaro na zaman lafiya da batun sauyin yanayi da kuma yanayin siyasar da ake ciki a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

Sanarwar wadda ta bayyana taken taron a matsayin, hanzarta aiwatar da tsarin kasuwanci maras shinge na nahiyar Afirka, ta kuma bayyana cewa, shugaban zai halarci wani taro na musamman na shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma da za a yi a gefen babban taron na AU.

Kakakin ya ce taro na farko da zaa yi shi ne na kwamitin tsaro na shugabannin ƙasashen ƙungiyar a kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo, wanda shugaban Afirka ta Kudu zar jagoranta a matsayinsa na shugaban kwamitin a watan Fabarairu.

”Sai kuma taro na biyu na kwamitin shugabannin ƙasashe da gwamnatoci a kan sauyin yanayi wanda shugaban Jamhuriar Nijar ke jagoranta a yanzu.” in ji sanarwar

Shugaba Buharin wanda zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati zai koma najeriya ranar Litinin 20 ga watan nan na Fabarairu, kamar yadda sanarwar ta ce.

Leave a Reply