Shugaba Buhari zai tafi Chadi bikin rantsar da Shugaba Mahamat Idriss Deby

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Chadi a yau Litinin don halartar rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Jamhuriyar Chadi na tsawon shekara biyu.

Za a yi bikin rantsuwar ne a N’Djamena, babban birnin ƙasar, inda za a tattauna kan batun mayar da ƙasar turbar dimokradiyya, bayan mutuwar tsohon shugaban Idriss Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, wanda aka kuma sani da Mahamat Kaka, ɗa ne ga marigayi shugaban Chadin Idris Deby.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Garba Shehu, mai taimaka wa Buhari kan yaɗa labarai, ta ce shugaban zai koma birnin Abuja, bayan kammala bikin rantsar da shugaban na Kasar Chadi.

Leave a Reply