Shugaba Buhari Zai Halarci Taro A Saudiyya

Fadar shugaban kasa tace Buhari zai je birnin Makkah ne domin ya halarci taron kungiyar musulunci na duniya.

Taron karo na goma sha hudu zai gudana a gobe juma’a 31 ga watan Mayu karkashin sarki Salman Bin AbdulAziz Al Saud inda kuma shugabannin kasashe zasu halarta.

A jawabin sakatariyar kungiyar, taken taron shine ‘ taron Birnin Makkah mai alfarma;  hada hannu dan cigaba’. Taron dai zai samar da wata matsaya game da al’amuran da suka shafi duniyar musulunci.

A jawabin da mai baiwa shugaban kasa shawara akan kafafen yada labarai, Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari yace zai gana da shugabannin kasashe daban daban.