Shugaba Buhari yayi kira ga maza a kan harkokin zabe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi kira ga maza da su kasance masu taimakawa wajen kyautata harkokin dimukradiyya ta hanyar bada gudunmawa wajen kada kuri’a a zaben shekara ta 2023 da ke karatowa.
Shugaban kasar yayi wannan kiran ne a daidai lokacin da ake bikin ranar maza ta duniya, wadda aka ware ta domin nuna hakkokin da suka rataya a wuyan maza.
Shugaban ya kuma yi kira ga maza da su kasance masu bin dokokin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shimfida a yayin gudanar da harkokin zabe.