Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su razana da sanarwar Amurka da Birtaniya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankulansu sakamakon gargadin da ofisoshin Jakadancin Amurka da Birtaniya suka gabatar na yuwuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja.

Buhari wanda ya koma Najeriya yau bayan tafiyar da yayi zuwa kasar Koriya ta Kudu, ya bukaci hukumomin tsaro da sauran jama’a da su sanya ido akan abubuwan dake faruwa kusa da su domin kare lafiyarsu.

Shugaban wanda yace sanarwar da gwamnatocin kasashen suka gabatar ba wai ya tabbatar da kai hari a birnin Abuja bane, saboda haka ya dace mutane su kwantar da hankalinsu domin kuwa jami’an tsaro sun tsaurara matakan da suke dauka tun bayan harin gidan yarin Kuje a watan Yuli.

Sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu, ya rabawa manema labarai tace Najeriya bata banbanta da wasu kasashen duniya da ake gabatar da irin wannan gargadi akansu ba, kuma Amurka da Birtaniya sun bada irin wadannan sanarwar akan wasu kasashen yammacin duniya dangane da abinda ya shafi barazanar kai harin ta’addancin.

Leave a Reply