SHIRIN AGILE YA SHIRYA TARON RANAR ‘YAYA MATA TA DUNIYA A KANO.

A kowacce shekara akan gudanar da gangamin wayar da kan al’umma kan mahimmacin  ‘ya’ya mata ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce Ranar 11 ga watan Oktoban kowacce shekara.

An fara kirkirar wannan rana ta ‘ya’ya mata ne kan dubban kalubalalen da suka dabaibaye rayuwar ‘ya mace a sassa daban-daban na duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa, sama da ‘ya ‘ya mata milyan 10 ne ke fama da barazanar auren wuri a sassa daban-daban na duniya. Kazalika annobar Covid 19 ta jefe ‘ya’ya mata cikin mawuyacin hali kama daga batun auren wuri da kuma cin zarafin mata.

Kididdiga ta bayyana cewa Yara mata kimanin kaso 72% na fama da barazanar cin zarafi, yayinda takwarorinsu maza kaso 66% ke fama da barazanar ayyukan bauta!

Ta fagen ilmi yara mata kaso 15% ne basa samun ilmin kimiyya da fasaha harma da lissafi a biyu bisa uku na kasashen duniya.

A Kano, Najeriya, Shiri tallafawa ilmin ‘ya’ya mata na AGILE karkashin bankin duniya, ma’aikatar ilmi ta jihar Kano da ta tarayya sun bujiro da tsarin tallafawa ilmin ‘ya’ya mata a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano.

A wannan rana ta 11 ga watan Oktoba, shirin AGILE ya bi sahun kungiyoyi masu zaman kan su, daidaikun al’umma, gwamnatoci wajen wayar da kan al’umma kan bawa ‘ya mace ilmi.

A yayin gudanar da taron a Kano wakiliyar Guarantee Naja’atu Danjuma Shuaibu, ta tuntubi Dr. Kabiru Shehu, Mai bawa Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje,  shawara kan ilmi kyauta kuma wajibi, ya bayyana cewa ‘mata na da matukar tasiri kan samar da ginanniyar al’umma’.  

Kungiyoyin kasa da kasa dake aiki a bangaren ilmi sun gabatar da Makala a wajen taron da suka gadar da HILWA, GEP, FIDA, Bridge Connect da kuma IWEI.

Leave a Reply