Shelkwatar Tsaron Najeriya Na Nema Wasu Mutane Su Takwas (8) Kan Zargin Kisan Sojoji A Jihar Delta

A ranar 14 ga watan Maris ne aka kashe jami’an soji 17 a wani samame da ya auku a yankin.

Wadanda ake nema ruwa a jallo sun hada da Ekpekpo Arthur, farfesa a fannin kimiyyar lissafi a jami’ar jihar Delta; Akeywiru Omotegbono, Andaowei Bakrikri, Igoli Ebi, wata mace; Akata David, Sinclear Oliki, Clement Oghenerukevwe da kuma Reuben Baru.

Sunayen sojojin da suka rasu sune A.H Ali, D.E Obi, S.D. Ashafa, U. Zakari, Yahaya Saidu, Danbaba Yahaya, Kabir Bashir, Abdullahi Ibrahim, Bulus Haruna, Sole Opeyemi, Bello Anas, Alhaji Isah, Clement Francis, Abubakar Ali, Adamu Ibrahim, Hamman Peter, da Ibrahim Adamu.

Bayan kashe jami’an soji, shugaba Bola Tinubu da babban hafsan soji sun yi alkawarin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

A ranar Laraba ne aka yi jana’izar sojojin a makabartar sojoji da ke Abuja, kuma daga bisani shugaba Tinubu ya karrama su da karramawar kasa. Shugaban ya kuma bayar da tallafin karatu ga ‘ya’yan marigayin.

Da yake jawabi yayin bikin jana’izar, Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojin kasar (COAS), ya ce abin takaici ne matuka yadda wadanda sojojin ke kokarin karewa sune suka kashe sojojin.

Babban hafsan sojin ya kara da cewa, an kwashe sama da sa’o’i 72 ana bincike domin gano muhimman gabobin wasu sojojin da suka mutu. Har ila yau, ya kara da cewa sojojin Najeriya sun “tsananta sosai” wajen neman makamai da sassan jikin sojojin da suka mutu da wadanda suka bata.

Hafsan sojojin ya kuma ce wasu daga cikin matan na jami’an da aka kashe na da ciki.

Leave a Reply