Shedu na cewa Yarima Mai Jiran Gado na kasar Saudiyya, Mohammed Bin Salman nada hannu a kissan Jamal Kashoggi

 An samu kwararan shaidu da ke nuna cewa Yarima Mai Jiran Gado na kasar Saudiyya, Mohammed Bin Salman da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar na da hannu a kisan Jamal Kashoggi.
Wani rahoton wata mai bincike ta majalisar ta dinkin duniya, Agnes Callamard, ya ce shaidun da aka samu na nuna bukatar gudanar da bincike na gaskiya.
Wasu jami’an kasar Saudiyya ne dai suka kashe Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Hukumomin Saudiyyar sun kafe cewa ba Yarima Bin Salman ne ya ba su umarni ba.
Tuni dai Saudiyya ta fara yi wa mutum 11 shari’a a asirce kan kisan Khashoggi, inda hukumomin ke son yanke wa mutum biyar daga ciki hukuncin kisa.
To sai dai misis Callamard ta ce shari’ar ta saba da ka’idodjin kasa da kasa, inda ta nemi da a dakatar da ita.