Shahararren Dan Wasan Kwaikwayon Barkwanci na Nollywood a Najeriya, Mr Ibu ya rasu

John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu ya rasu bayan ya sha fama da jinya.

Mista Ibu ya rasu ne ranar Asabar a wani asibiti da ke birnin Legas inda yake jinya.

Shugaban kungiyar taurarin fim ta Najeriya, Emeka Rollas ya tabbatar da labarin rasuwar ta Mista Ibu a ranar ta Asabar.

Ya bayyana shafinsa na instagram cewa: “Cikin matukar jimami ina sanar da cewa Mista Ibu ya rasu. Mai kula da lamuran marigayin ya ce Ibu yi fama da ne da wani nau’in ciwon zuciya na tsawon shekara 24”.

Rashin lafiyar Mista Ibu ta tsananta ne a 2023, duk da likitoci sun ta fafutikar ceto rayuwarsa.

A cikin watan Oktoban 2023 ne wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga dan din na neman masoyansa su saka shi cikin addu’a.

A cikin bidiyon, Mista Ibu ya ce ya kwashe tsawon lokaci yana jinya a asibiti sanadiyyar wata cutuka “wadda ba a gane kanta ba”.

A cikin bidiyon ya ce likitoci sun bayar da shawarar yanke kafafunsa.

Ya kara da cewa “A yanzu haka ina ci gaba da jinya a asibiti, shugaban asibitin ya ce abin da ya fi shi ne a yanke kafata matukar abin da za su yi bai cimma nasara ba”.

Daga nan ya bukaci masoyansa su yi masa addu’a kada a yanke masa kafa.

John Okafor wanda ya kasance dan wasan kwaikwayon barkwanci na dabe ne a jihar Enugu da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ya fito a cikin daruruwan fina-finan Nollywood a ciki da wajen Najeriya.

Ya shahara kan yadda yake sarrafa fuskarsa a lokacin da yake son bai wa masu kallo dariya.

A lokuta daban-daban kuma yakan yi rawa da raha domin nishadantar da masu kallo.

A cikin watan Disamban 2023, iyalan Mista Ibu suka yi bayani kan rashin lafiyar tasa.

Inda labari ya rika yawo kan cewa an yanke dukkanin kaffuwan Mista Ibu guda biyu.

Sai dai daya daga cikin iyalansa mai suna Valentine Okafor ta bayyana a shafinsa na instagram cewa har ya zuwa lokacin kafa daya aka yanke wa Mista Ibu.

Iyalin sun kuma fayyace gaskiya game da rashin lafiyar tasa, inda suka ce ba ciwon suga ne yake fama da shi ba, sai dai “yana yawan samun curewar jini a bangaren kafafunsa (lalacewar jijiyar jini)” da kuma wasu cututtuka da ke barazana ga rayuwarsa.

Leave a Reply