Savannah ta bukaci gudanar da zabe mai nagarta a 2023

Kungiyar nan dake rajin tabbatar da cewa an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ta Savannah Community Forum dake nan Kano, ta bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar zabe da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gudanar da zaben shekara  2023 cikin nasara.

Mukaddashin shugaban kungiyar Malam Ahmad Sani Hanga, shi ne ya furta hakan a yayin zaman yaukaka dangantaka tsakanin kungiyar ci gaban al’umma ta Savannah da kafafen yada labarai anan Kano.

Daga bisani ya yi karin haske kan aikin da ya rataya a wuyan al’umma musamman kungiyoyi masu zaman kansu wajen ganin an bibiyi yadda aka gudanar da zabe da kuma bayan zabe wajen tabbatar da cewa ‘yan siyasa sun cika alkawarin da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun jaddada bukatar da ke akwai na tafiya kafada da kafada da manema labarai wajen ganin kowa ya bada gudummuwa wajen gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2023.

Leave a Reply