Satar amsa lokacin jarrabawa babbar matsala ce a Najeriya – Ministan Ilimi

Ministan ilimi na Najeriya Adamu Adamu ya buƙaci hukumomin shirya jarrabawa a Najeriya da su yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar satar amsa lokacin jarrabawa.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin buɗe taron tattaunawa kan yadda za a magance satar amsa, wanda majalisar dokokin Najeriya da hukumar shirya jarrabawa ta ƙasa (NECO) suka shirya a  jihar Legas.

Ministan ya bayyana satar amsa lokacin jarrabawa a matsayin  babbar matsala wadda ke illa ga yadda hukumomi ke shirya jarrabawa a Najeriya wanda hakan ke mayar da kasar koma baya wajen magance satar amsa.

Ya ƙara da cewa ya zama wajibi a yi amfani da fasahar zamani wajen ganin an tsaftace harkar jarrabawa ta ƙasar.

Leave a Reply