Sarkin Musulmi Ya Koka Kan Rashin Aiwatar Da Hanyoyin Magance Matsalolin Arewa

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce jagororin Arewacin Najeriya sun san hanyoyin da za a magance matsalolin tsaro da talauci da suka addabi yankin, amma ba sa kaddamarwa a aikace.

Sarkin Musulmin ya shaida wa taron sarakuna da jagororin Arewa cewa matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi da kuma talauci musamman a tsakanin matasan Arewacin Najeriya babbar barazana ce ga kasar.

Da yake jawabin a taron da suka gudanar a jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Sa’ad ya bayyana cewa a halin yanzu ’yan Najeriya a fusace suke saboda fama da yunwa da talauci, bugu da kari ga kuma durkushewar harkokin samun kudi da sana’o’i.

A bangaren sa, shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS, Yusuf Magaji Bichi wanda daraktan hukumar na jihar Kaduna Abdul Enenche ya wakilta, ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya sakamakon irin rawar da suke takawa wajen dakile barazanar tsaro tun kafin a kai ga aikata su.

Leave a Reply