Sarkin Kano na 14 yace Kayyade kudaden da za a cire a kullum zai fi shafar ‘yan siyasa ne ba talakawa ba

Khalifa Muhammad Sanusi, ya ce matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na takaita cirar kudade zai fi yin tasiri ne  a kan `yan siyasar kasar nan fiye da talakawa.

Ya bayyana hakan ne a karshen karatun Madaris da ya saba yi duk karshen mako.

Ya ce `yan siyasar Najeriya na amfani da kudi a lokacin zabe don sayen kuri’un jama’a, lamarin da ke haifar da koma-baya ga kasar nan.

Muhammadu Sanusi na II ya ce abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar al’umma, suna barin mutane a cikin wahala da yunwa, sannan su fito da irin kudaden su sayi kuri’u, su biya ‘yan sanda, da DSS, da ma’aikatan INEC da `yan daba a sayo musu kwaya, a saya musu makamai, don hana mutane zabe.

Haka kuma Sarkin Kanon na 14 ya ce wannan tsari da CBN ya fito da shi, shi ne zai fara rage barnar da ‘yan siyasa ke yi kuma zai takaita magudin zabe a kasar nan

Dokar takaita cirar kudin da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fitar a ranar 6 ga watan Disambar da muke ciki, za ta fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2023.

Leave a Reply