Sarkin Gwandu yayi mubaya’a ga Sarkin Kano Sanusi na II

Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar, Muhammad Iliyasu Bashar (mai ritaya) ya aike da sakon taya murnar hawa karagar mulkin Kano zuwa ga mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.


Wannan ya biyo bayan mayar da Sarki Sanusi na II da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yayi, biyo bayan rushe dokar da ta kafa sarakuna biyar da majalisar dokokin Kanon tayi.

Sarkin Gwandu ya taya Sarki Sanusi murnar dawowa karagar mulkin masarautar Kano tare da fatan gamawa lafiya.

Leave a Reply