Tsohon dan wasan kwallon kafa na Kamaru Samuel Eto’o zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafar Kamaru (Fecafoot).
Tsohon dan kwallon na Barcelona da Inter Milan ya sanar da hakan a shafukansa na sada zumunta a ranar Talata da yamma, yana cewa ya dauki matakin ne “saboda soyayyar da yake yi wa Kamaru da kwallon kafa.”
“Lokaci yana kurewa. Ba za mu iya jira ba. Lokaci ya yi da za mu gina harkar kwallon kafarmu,” in ji Eto’o.
Ana sa ran za a yi zaben hukumar kwallo ta Fecafoot ranar 11 ga Disamba, inda za a fara wasannin Gasar Kofin Afirka a Kamarun ranar 9 ga watan Janairun 2022.
Fecafoot ba ta sanar da cewa za ta saki jerin sunaye na karshe na ‘yan takarar shugabancin hukumar.
Eto’o mai shekara 40, fitaccen dan wasa ne, inda ya sha yin nasara a gasanni na cikin gida da na Turai a Spaniya da Italiya.
Dan wasan wanda ya ci zaben dan kwallon Afirka da ya fi kowa sau hudu ya zura kwallo 56 a raga ya kuma ci wasanni 118 sannan ya yi zarra ma a gasar Firimiyar Ingila a Chelsea da Everton, inda ya kawo karshen aikinsa a Qatar.
A matakin wasanni na duniya kuwa, ya taimaka wa Kamaru ta ci Gasar Kofin Afirka a 2000 da 2002 sannan ya ciyo kambun zinare a Gasar Olympic ta Sydney 2000.