Sama da yara milyan 1.5 ne ke barazanar fadawa hadari sakamakon ambaliyar ruwa a Nigeria-UNICEF.

MUSA TIJJANI AHMAD

Sama da yara milyan 1.5 ne ke barazanar fadawa hadari sakamakon ambaliyar ruwa a Nigeria.

Wani rahoton hukumar yara ta duniya UNICEF ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya bayyana cewa kimanin mutum milyan 2.5 na bukatar agajin gaggawa, inda kaso 60% yara ne! da ka iya kamuwa da cututtuka masu saurin yadawa da kuma hadari ga lafiyar yaran.

Hukumar ta UNICEF ta nuna fargabar ta  kan wannan yanayi da aka shiga a kasar nan; inda ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 34 daga cikin 36 a kasar nan, yayinda mutum sama da milyan 1.3 suka rasa muhallansu.

Rahoton ya nuna cewa mutum sama da 600 ne suka mutu yayinda gidaje sama da 200,000 ne suka lalace ko kuma aka yi asarar su baki daya.

A jihohin arewa maso gabas da suka hadar da Borno, Adamawa da Yobe kadai an samu bullar kwalara  7,485 yayinda aka samu rahoton mutuwar kimanin 319 a rahoton 12 ga watan Oktoba. Hasashen masana yanayi ya bayyana cewa za’a cigaba da samun ruwan sama a don haka akwai bukatar agajin gaggawa, domin gudun sake afkawa ibtila’i.

A wabi daftarin hukumar kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF wato (CCRI)  a takaice, ta ce Najeriya na daga cikin kasashe mafi hadari ta fuskar tasirin sauyin yanayi, inda rahoton ya bayyana cewa Najeriya ce kasa ta biyu daga cikin kasashe 163! Yara kanana na cikin barazanar fuskantar kalubalen sauyin yanayi, karancin abinci mai gina jiki, tsabtataccen ruwan sha, ilmi, kiwon lafiya da sauransu.

Leave a Reply