Sadiya Farouq: An yi min cushen naira biliyan 206 a kasafin kuɗin ma’aikatata

OTHER

Ministar ma’aikatar jin-ƙai ta Najeriya Sadiya Umar Faruq ta yi zargin cewa an yi mata cushen naira biliyan 206 a kasafin kuɗin ma’aikatarta.

Yayin wani zaman kwamitin kula da ayyuka na musamman na majalisar dattawan ƙasar nan, Sadiya Farouk ta nisanta kanta da zunzurutun kuɗin da ta ce an cusa a kasafin kuɗin ma’aikatar tata na  shekarar 2023.

Sanata Elisha Abbo wanda mamba ne a kwamitin ya tambayi ministar game da kudin.

Ta ce za su nemi bayani dalla-dalla daga ma’aikatar kuɗi kan yadda aka yi kuɗin ya ninka haka, duk da a baya ma ba a saki kuɗin domin yin ayyukan ba. Saboda haka za su ji daga gare su sai su koma su basu  bayani.

A kan hakan ne kwamitin ya ce zai gayyaci ministar kuɗi da kasafi, Zainab Ahmed domin ta bayar da bayani kan kuɗin naira biliyan 206 da Sadiya Farouq ta nisanta kanta da su.

Leave a Reply