Sadiq Ango Abdullahi ya lashe zaɓen majalisar wakilai

Sadiq Ango Abdullahi, ɗaya daga cikin mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su bayan kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, ya lashe zaɓen ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Tun farko, takarar Sadiq Ango ta ja hankalin al’umma ne bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani a lokacin da yake hannun ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da ƴan bindiga suka sace a lokacin da suka kai wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna hari a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa Sadiq, wanda ya yi takara a jam’iyyar PDP, ya samu ƙuri’a 33,616, wanda ke biye masa na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 31,737, sai kuma jam’iyyar NNPP mai ƙuri’a 2,368.

Ya wallafa a shafinsa na tuwita, lokacin da jami’in hukumar zaɓe ke sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Leave a Reply