Sabuwar Gwamnati Da Za’a Kafa Zata Banbanta Da Na Yanzu – ‘Yan Najeriya

Tun bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya da hukumar INEC ta yi a makon jiya ne ‘yan kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan irin hasashen fa fatar da suke da shi ga zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Suna son ganin yadda zai gano bakin zare warware muhimman batuttuwan da suka addabi kasar a fuskoki daban-daban. A yayin da wasu ke tsokaci a kan irin bambance-bambancen da za’a iya gani a tsakanin shugaba Buhari da kuma zababben shugaba Bola Tinubu.

Wasu kuma na dasa alamar tambaya a kan cewa shin ko Tinubu zai iya tabuka wani abin a zo a gani na daban la’akari da cewa a yanzu jam’iyyarsa ke kan karagar mulk, shin za a iya samun sauye-sauye da za su kai ga ci gaba ga kasar a bangarori daban-daban?

Mun yi nazari a kan ababen da ‘yan kasar ke cewa a game da wadannan tambayoyi.

Batun irin zato ko fata da ‘yan Najeriya ke da shi a kan zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed da kuma tsokaci a irin salon shugabanci da zai yi amfani da shi na ci gaba da jawo muhawara a tsakanin ‘yan kasar inda ake samun mabambantan ra’ayoyi.

Wasu na kyautata zaton cewa shi Tinubu zai iya tabuka abin a zo a gani wasu kuma na shakku a kan abin da za’a gani idan aka kafa sabuwar gwamnati.

Malama Lami Sumayya Murtala, ma’aikaciya ce kuma daya daga cikin iyaye mata da suke fafutukar ganin an inganta tsarin ilimi da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, ta ce kamata ya yi zababben shugaban kasa Tinubu ya duba abubuwan da suka faru a wannan gwamnatin, wanda yake ganin ana kuka da su ya taimaka ya farfado da abubuwan da suke faruwa.

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa, a zaben wannan karon, matasa ne suka fi fitowa kada kuri’ar su don ganin an sami sauyi mai ma’ana a shugabancin kasar.

Yusufudeen A. Yusuf ya ce za’a ga banbanci akan tattalin arziki da saura muhimman bangarori.

A halin da ake ciki yanzu masana a fannin tsare-tsaren gwamnati na cewa ko mai ya faru da sakamakon da aka samu nan gaba a game da korafe-korafen saura ‘yan takarar shugaban kasa da aka fafata da su a zaben na watan Febrairu wato jam’iyyut Leba da PDP, gwamnatin da za’a kafa a watan Mayun na da jan aiki a gabanta.

Leave a Reply