Sabon Gwamnan Bauchi ya bayyana Takaici game da sashen lafiya

Sabon gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya bayyana takaicinsa game da halin da sashin lafiya ke ciki a jihar.

Mohammad ya bayyana hakan ne jim kadan bayan an rantsar dashi a matsayin gwamna na shida tare da mataimakinsa Baba Tela a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake garin Bauchi.

Babbar jojin jihar, Rabi Umar ce ta jagoranci rantsuwar kama aiki ga gwamnan tare da mataimakinsa.

Bala Muhammad Sabon gwamnan Bauchi

Tsohon ministan Abujan yace likitoci arba’in da hudu ne kawai a jihar wanda ke nuna cewa likita guda daya ne zai kula da akalla mara sa lafiya dubu dari da hamsin.

Mohammad ya kuma koka game da halin da bangaren ilimi ke ciki inda yace  akwai yan makaranta yara miliyan daya da dari uku da basa zuwa makaranta.