Bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa daga ranar daya ga watan Disamba duk wani ma’aikacin gwamnatin ba za a bar shi ya shiga ofis ba sai ya nuna shedarsa ta yin rigakafin korona ko kuma shedar ba ya dauke da cutar, ma’aikata da dama na bayyana ra’ayoyin daban-daban.
Sakataren Gwamnatin wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa kan yaki da korona Boss Mustapha ne ya sanar da matakin a yayin zaman ƴan kwamitin a Abuja ranar Laraba 13 ga watan Oktoba 2021.
Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa ” daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma’aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce sa’a 72 ba kafin su shiga ofis.”
A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdigar gwaji ta sama da makonni hudu da suka wuce ta nuna cewa yayin da bazuwar cutar ke raguwa a wasu jihohi, tana karuwa ne a wasu jihohin.