Rundunar ‘Yansandan Najeriya Ta Haramta Amfani Da Na’urar POS A Daukacin Ofisoshin Ta

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta haramta amfani da na’urar cirar kudi ta POS a daukacin ofisoshin ta dake fadin kasar.

Wannan na kunshe ne cikin wani sako da mai magana da yawun rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, wanda yace an dauki matakin ne biyo bayan samun korafe korafe daga al’umma na cewa wasu batagarin jami’an ‘yan sanda na amfani da na’urar wajen aikawa ko cire kudi ba bisa ka’ida ba.

Kazalika yace matakin zai taimaka wajen dakile yawaitar cin hanci da rashawa, da kuma tabbatar da tsafta a tsarin aikin dan sandan Najeriya.

Haka kuma ya gargadi daukacin jami’an da su kauracewa duk wani abu da zai jawo musu zubewar kima da mutunci.

Leave a Reply