Rundunar yansandan Jigawa ta cafke matasa 2 kan satar gadaje a sakandiren Malammadori

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta tabbatar da nasarar kama wasu mutane da ake zargin bata gari ne, kan laifin shiga makarantar sakandiren gwamnati ta hadaka dake garin Malammadori a jihar, bayan da suka tafi kaitsaye zuwa dakin dalibai suka kwashe gadaje 19 da katifu 4.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Lawan Shisu Adam, wanda ya bada wannan tabbaci ta cikin wata sanarwa daya aikowa Guarantee Radio a karshen mako, yace a lokacin da labarin ya zo musu sun baza jami’ansu, inda suka yi nasarar cafke mutanen biyu, da kayayyakin da suka sace.

DSP Shisu Adam yace a lokacin da suke tattaunawa da su ake bincikar su sun tabbatar da aikata wannan laifi na sata da suka yi.

Hakazalika yace jami’ansu dake karamar hukumar Babura, sunyi nasarar kama wasu yara guda biyu, da suka haura gidan wata baiwar Allah, suka sace mata hatsinta da kuma kudi sama da Naira dubu 40, wanda yace anyi nasarar kama wadannan yara da ragowar hatsi da ragowar kudin, duk da dai sun bayyanawa ‘yansandan cewa: akwai wajen wacce suke kaiwa kaya idan sun sata, kuma tini bincike yayi nisa wajen ganin an kamo wannan baiwar Allah da take siyan kayayyakin sata.

Leave a Reply