Rundunar ‘yansanda za ta gudanar da bincike kan zargin kaiwa tawagar PDP hari a Maiduguri

Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa zasu gudanar da cikakken bincike dangane da zargin kaiwa tawagar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, hari a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Babban Sufetan, ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Alkali Baba, na wannan jawabi ne a yayin da yake amsa tambayoyi kan hare-haren ta’addanci da aka kaiwa ayarin Atiku Abubakar a jihohin Kaduna, Rivers da kuma Borno, inda ya ce kakakin rundunar yan sandan jihar Borno ya yi gaggawar yanke hukunci kan wannan al’amari dake bukatar zurzurfan bincike!

Ya ce a halin yanzu sun kafa kwamiti kwararru da zasu gudanar da bincike kan wannan al’amari.

Idan dai za’a iya tunawa a ranar larabar da ta gabata ne wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka kaiwa ayarin Atiku Abubakar hari a birnin Maiduguri.

Leave a Reply