Rundunar ‘yansanda ta Kasa ta taka-rawa a karashen zaben gwamnan a jihar Kano” Hajiya Naja’atu Bala Muhammad

Rundunar ‘yansanda ta Kasa ta taka-rawa a karashen zaben gwamnan a jihar Kano, adon haka akwai bukatar su kauracewa shiga sabgar ‘yan siyasa musamman a wannan zango
na mulkin shugaba Muhd Buhari, da yake matukar bukatar tallafi a bangaren tsaro.

Hajiya Naja’atu Muhammad ce ta bayyana hakan a wata takarda da ta fitar , inda tace lokaci yayi da ya kamata a yiwa bangaren tsaro garambawul domin tunkarar kalubalen dake addabar Kaarnan.

Naja’atu Muhd, wacce kwamishinace a hukumar kula da rundunar ‘yan sanda ta Kasa, tace sakamakon rauni daga wasu jami’an yansanda ne yasa dakarun sojin Kasarnan suka siga al’amuran da suka shafi tsaron cikin gida domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.