Rundunar yan sandan jihar kano ta kubutar da mutane 47 daga wani gidan horas da kangararru da ke aiki ba bisa kai’da ba a unguwar ‘yar Akwa dake karamar hukumar tarauni a jiharnan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ,shine yabayyana hakan ,inda yace wadanda suka kubutar ,gabadayansu mazane wanda suke tsakanin shekaru 12 zuwa shekara 30.
Yace gabadayansu anmika su asibitin kula da marasa lafiya na murtala muhammed domin duba lafiyarsu , sakamakon dukkaninsu suna dauke da raunuka a jikinsu ,dalilin dukansu da akeyi a gidan horas da kangararru wanda suke aiki ba bisa kaidaba .
Kazalika ya kara dacewa rundunar ta su ta kama biyu daga cikin masu kula da gidan ,inda yace zasu gudanar da bincike akan hakan .