Rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane 11

Rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane 11 a wasu yankunan karamar hukumar Kankara dake jihar sakamakon hare haren da batagari suka kai.

Mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isa ne ya tabbatar da mutuwar mutanen.

Rahotanni sunce mutane 16 ne aka yiwa kisan gilla a karamar hukumar Danmusa sai dai yan sanda basu tabbatar da adadin ba.

Tuni sarkin Katsina, Dakta Abdulmumin Kabir ya jagoranci mambobin masarautar Katsina wajen yin jana’izar mamatan da suka mutu sakamakon hare haren da batagari suka kai.