Rundunar yan sanda a Abuja sun tsare sanata Elisha Abbo bisa zarginsa da cin zarafin wata mata

Rundunar yan sanda a Abuja sun tsare sanata Elisha Abbo bisa zarginsa da cin zarafin wata mata a wani shago dake babban birnin tarayya.

Kwamishinan yan sanda na garin Abuja Mr Bala Ciroma ne ya bayyanawa manema labarai a yayi zantawar su ta wayar tafi da gidanka inda yace an tsare sanatan ne har sai an kammala bincike akan zargin da ake masa na cin zarafi.

An dai hangi Abbo, wanda ke wakiltar Adamawa ta arewa a wani shago a faifan bidiyo yana cin zarafin wata mata kamar yadda jaridar nan ta premium times ta rawaito.

A hango shi yana dukan matar ne bayan wacce take bashi hakuri akan kar ya ci zarafin mai shagon wadda a cewarsa take ci masa fuska.

Bidiyon da ya watsu a duniya ya tunzura yan Najeriya inda suka yi kira ga hukumomi da majalisar dattawa data ladaftar da shi.