Rundunar sojin Najeriya ta zaburar da dakarunta kan dabarun yaki da ta’addanci
Rundunar sojin Najeriya ta yaye sabbin dakarunta na musamman kan dabarun yaki da matsalar tsaro a kasar, bayan shafe tsawon watanni suna daukar horo na musamman a cibiyar horas da sojoji dake Kachia a jihar Kaduna.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Brigediya Janaral Onyema Nwachukwu ya fitar a Abuja.

Yace rukunin wadanda aka baiwa horon na cikin tawagar sojojin da aka yaye bada jimawa ba, domin magance matsalolin tsaro da samar da sauyi kan tsarin yadda ake bada tsaron a Najeriya.
Da yake jawabi gaban dakarun sojin da aka yaye, babban hafsan sojin Najeriya Lafatanal Janar Taoreed Lagbaja, yace manufar rundunar sojin akan shirin bayar da horon shi ne ta kara matsa kaimi wajan nazartar gibin da ake samu a aikace aikacen ta, ta hanyar bayar da irin wannan horo.
Taoreed Lagbaja ya kuma godewa shugaba Bola Ahmad Tinubu, kan cikakken goyon bayan da yake baiwa rundunar soji hadi da ministan tsaro Mohammed Badaru, da ma babban hafsan tsaro na kasa Janaral Christopher Musa, kan kokarin su na kawo cigaba mai ma’ana a aikace aikacen rundunar sojin, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.