Rundunar ƴan sandan Kano ta kama masu sata da sayar da yara

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar kama wani gungun mutanen da suka ƙware wajen satar yara da kuma safararsu zuwa waɗansu jihohi a kudancin Najeriya.

A wata hira da ya yi da BBC, mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa, ƴan sandan sun yi nasarar cafke wasu ‘yan ƙungiyar da dama, waɗanda ke gudanar da miyagun ayyukan nasu a tsakanin jihohin Kano da Bauchi da Anambra da Imo da kuma Legas.

Ya ce, a ranar 15 ga watan nan na Disamba, 2023, an kama wata mata mai suna Comfort Amos, mai shekara 45, a tashar manyan motocin safa da ke Mariri a Kano a lokacin da take ƙoƙarin jigilar wani yaro, Abdulmutallib Sa’ad mai shekara biyar zuwa jihar Legas.

An gano cewa an sace Abdulmutallib ne a ranar 12 ga Disamba, 2023, daga ungwar Zango Quarters da ke jihar Bauchi.

Binciken da aka gudanar ya kai ga kama wasu da dama da suka haɗa da Chika Ezugbu da Joy Nzelu da Clement Ali da Emeka Ekeidigwe, dukkansu mazauna Kano, waɗanda ake zarginsu da hannu a cikin ayyukan ƙungiyar.

”A halin yanzu mun kamo mutane guda tara, kuma an samu yara guda bakwai a wurinsu waɗanda shekarunsu na haihuwa daga uku ne zuwa shekara takwas” in ji shi.

SP Kiyawa a ƙara da cewa, ‘yaron da aka fara samu, Abdulmutalib Sa’ad wanda har an sauya masa suna zuwa Ifeanyichukwu an sayar da shi ne kan kuɗi N480,000, kuma daga shi an sami wata yarinya mai suna Asiya Mukhtar, wadda aka sauya mata suna zuwa Chioma ita kuma an sato ta ne daga jihar Bauchi kuma ita ma an sayar da ita ne kan wannan farashin na N480,000, kuma a halin da ake ciki suna hannun ƴan sanda kuma ana gudanar da bincike bisa ga umarnin kwamishinan ƴan sandan jihar,’

Rudunar ta bayyana cewa an gano iyayen akasarin yaran da aka ceto, waɗanda a halin yanzu suke cikin ƙoshin lafiya.

SP Kiyawa ya ce waɗanda ake zargin suna hannun ƴan sanda kuma ana kan gudanar da bincike kan lamarin

‘Mun kama duka ɓangarorin, da masu satowar da masu siya a wurinsu su kuma sayar, ba wanda ba mu kama ba a kowa ne ɓangare, kuma sun yi mana bayanin yadda aka sayar musu da kuma kuɗin da suka siya’. In ji shi.

Leave a Reply