Rufe iyakokin Najeriya da Nijar na jawo mana asarar biliyoyin naira – Ƴan kasuwar Arewa

Iyakar Najeriya

Matakin da ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) ta dauka na sanya takunkumi da rufe iyakokin kasashen da Nijar ke maƙwabtaka da su sakamakon juyin mulki ya sa wasu ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya kukan yin asarar biliyoyin naira.

Kungiyar raya tattalin arzikin arewacin Najeriyar ta Arewa Economic Forum na cewa lamarin ya haifar da koma-baya ga harkokin ‘yan kasuwa, inda ta ce a duk mako yankin na asarar akalla naira biliyan 13 a sanadiyar rufe iyakokin.

‘Yan kasuwar sun ce idan har ba a dauki matakin gaggawa ba lamarin zai iya haifar da nakasu da koma-baya ga tattalin arzikin arewacin Najeriyar baki daya.

Mataimakin shugaban kungiyar, Muhammad Kantoma, wanda ya bayyana irin asarar da ake yi cikin tattaunawarsa da BBC, ya ce takunkumin ya sa al’ummar ƙasashen biyu sun daina amfana da harkokin kasuwancin kamar yadda suka saba.

‘’Akwai mutanenmu da ke shigowa da kaya ta iyakokin Nijar daga wasu kasashe tun lokacin da aka rufe boda, akwai akalla kwantenoni 2,000 da wani abu,’’ in ji Kantoma.

‘’Akalla karamar kwantena za ta yi dala 20,000, wata za ta kai dala 70,000. Saboda haka mu ga ya kamata wannan asarar da mutane ke yi mu yi kira domin gwamnati ta san abin da za ta yi,’’ a cewarsa.

Ita ma kungiyar masu shigar da kaya daga iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin ta koka da matakin rufe iyakar, inda wani daga cikin masu hada-hadar, Hamza Saleh Marini Jibiya, ya shaida wa BBC cewa yanzu haka akwai tarin kwantena a Kwatano fiye da 1,000, wadanda za a shigar arewacin Najeriya amma ba dama.

Ya ce akwai iyakar arewacin Najeriya da Kwatano ta yankin jihar Kebbi, kuma ita ma a rufe take, duk da cewa ba ta da iyaka da Nijar.

‘’Muna roko ga shugaban kasa da ya bayar da umarni a bude ta saboda haraji muke biya, wasu daga cikin kayan ma ba sa dadewa suke lalacewa,’’ in ji shi.

Ya koka da cewa a yanzu su ‘yan arewacin Najeriya ba su da wata iyaka da take a bude sabanin yankin kudu maso yammacin Najeriyar, wadanda ya ce suna da iyakoki wajen uku zuwa hudu a bude.

Daga cikin kungiyoyin da ke kokawa kan rufe iyakokin na arewacin Najeriya, akwai ta matasan yankin arewa maso gabashin kasar, wadda shugabanta Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham ya bayyana irin halin da matakin ya jefa al’umma a ciki musamman talakawa.

‘’Kulle wadannan iyakoki da aka yi da takunkumi da aka sanya mata [Nijar] ba gwamnati ba ce take danadana kudarta, talakawa ne suke dandana kudarsu a yanzu,’’ in ji shi.

Ya kara da cewa: ‘’Don haka muke kira ga musamman shugaban Najeriya da masu ba shi shawara da hafsoshin tsaro na Najeriya, don a warware bakin zaren.’’

Wani dan kasuwa Ahmed dayyabu ya ce a yanzu suna cikin fargabar asarar dimbin dukiya saboda yanayi da ake ciki na damuna, wanda ruwa zai iya lalata musu kaya da motoci ke dauke da su a iyakokin da ke rufe.

Ya ce kayayyakin sun hada da alewa da biskit da cingam da ashana da salatif, da sauransu, wadanda dukkaninsu kaya ne na miliyoyin naira da za su iya lalacewa da wuri.

Dan kasuwar ya ce bayan wadannan na kan iyakokin Najeriya, akwai kuma wadanda suke a kan iyakar Benin da Nijar, a garin Malanville na. “Mota ta fi dubu,” a cewarsa.

”Wannan fa bayan wadanda ma suke cikin tashar ruwa wadanda ba a ma fito da su ba ke nan.”

Tarin kungiyoyin sun yi gargadin cewa muddin gwamnatin Najeriya ba ta sauya shawara kan rufe iyakokin arewacin kasar ba, lamarin ka iya kara gurgunta tattalin arzikin yankin wanda kuma zai shafi sauran sassan kasar.

Farashin kaya na tashi

Matakin rufe iyakokin da kungiyar Ecowas ta dauka a kan Nijar din bayan juyin mulki, ya haddasa tashin farashin kayayyaki, kamar yadda wasu ‘yan kasuwar da abin ya shafa suka tabbatar wa BBC.

Alhaji Umar Ayuba Ƙwa dan kasuwa ne a Dawanau ta jihar Kano, ya ce a halin da ake ciki kudin kayayyaki sun tashi a can Nijar da ma kasashen da ba a iya shigar da kayan a yanzu, inda Najeriya na daya daga cikinsu.

“Kaya kamar taliya da gero, su ne jama’a suke ta fama da tashin farashinsu a dukkanin wadannan kasashe,” kamar yadda ya bayyana.

”Yanzu maganar da ake yi, ina kasuwanci ne a tsakanin Najeriya da wasu kasashe na yankin Ecowas, yanzu ina da garin kuka da diyan kalwa da ake daddawa da ita, wadda za a kai Nijar, daga can ma a wuce gaba.

”Can kuma daga Nijar din ina sayo wake da aya, yanzu maganar da nake ina da motoci a bakin iyakar Jibiya, kamar biyu ko uku, biyu wake ne, daya kuma ta dauko aya. Waken nan akalla ya kai kusan naira miliyan 25, ayar kuma ta kai miliyan 10 da wani abu, ba su samu tsallakowa ba.”

Ɗan kasuwar ya ce lamarin su ‘yan kasuwa da sauran talakawa yake shafa a don haka ya bukaci gwamnati da ta yi kokarin sasantawa a samu maslaha.

Leave a Reply