Ronaldo ya koma atisaye tare da ‘yan wasan Man United

Dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da ‘yan wasan kungiyar, bayan da aka umarce shi ya motsa jiki shi kadai a makon jiya.

Sabon kociyan United, Erik ten Hag ne ya dauki wannan matakin na ladabtar da kyaftin din tawagar Portugal.

Ronaldo mai shekara 37, bai yadda ya canji dan wasa ba a karawa da Tottenham a gasar Premier.

Hakan ya sa kungiyar ba ta je da shi buga wasan da ta tashi 1-1 da Chelsea ba a Stamford Bridge a Premier a karshen mako.

Daman Ten Hag ya ce sai ya hukunta Ronaldo kan abin da ya aikata, an kuma fahimci cewar kociyan da dan kwallon sun tattauna a tsakaninsu don dinke baraka.

Ronaldo bai bari an tashi da shi a fafatawa da Tottenham, wadda ya fice daga fili tun kan a tashi karawar.

Da yake ya koma atisayen, wasu na cewar watakila a saka shi a Europa League ranar Alhamis da United za ta kara da FC Sheriff a Old Trafford.

Haka kuma mai tsaron bayan kungiyar kyaftin, Harry Maguire da Donny van de Beek sun yi atisaye ranar Talata, bayan jinya da suka sha.

Leave a Reply