Ronaldo ya ci kwallo ta 700 a tarihin rayuwarsa a kungiyoyin da ya wakilta.

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 700 a tarihin kungiyoyin da ya buga wa tamaula, bayan da Manchester United ta doke Everton a Premier League.

Manchester United ta yi nasara a kan Everton da ci 2-1 a babbar gasar Premier  ta Ingila a Goodison Park, shi ne ya ci na biyun.

Everton ce ta fara cin kwallo a minti na biyar da murza leda ta hannun Alex Iwobi, minti 10 tsakani United ta farke ta hannun Antony.

Kwallon farko da dan wasan tawagar Portugal mai shekara 37 ya ci a gidan Everton tun bayan 2005.

Kwallo na biyu da Ronaldo ya ci a bana, wanda ya zura na farko a raga a Europa League da Sheriff FC, kuma na 699 da ya ci a lokacin cikin watan Satumba.

Ronaldo ya fara daga zaman benci a karawa da Everton ranar Lahadi daga baya ya canji Anthony Martial, wanda ya ji rauni a minti na 29.

Haka kuma Ronaldo yana gaban Messi a yawan cin kwallaye a kungiyoyin da yake buga wa wasanni, bayan da kyaftin din Argentina keda 691 a fafatawar da ya yi Barcelona da Paris St Germain.

Leave a Reply