Ronaldo ba zai buga wasa da Najeriya ba

Tauraron ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Portugal Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da ƙasarsa za ta fafata da Najeriya ba a yammacin Alhamis sakamakon ciwon ciki da yake fama da shi.

Kocin tawagar Portugal, Fernando Santos, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labaraia da aka yi ranar Laraba gabanin wasan na sada zumunta.

“Ba zai buga wasan [Najeriya] ba gobe [Alhamis]. Ya rasa ruwan jiki sosai saboda ciwon ciki da yake fama da shi kuma ba ya atasaye,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “yana ɗakinsa yana hutawa da kuma samun sauƙi”.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta fafata da Portugal a wasan share fagen gasar Kofin Duniya ta 2022 da za a fara a Qatar.

Za a buga wasan a Filin Wasa na José Alvalade da ke birnin Lisbon na Portugal ranar Alhamis da ƙarfe 7:45 agogon Najeriya da Nijar.

Najeriya ba ta samu gurbin shiga Kofin Duniya ba sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun babbar abokiyar hamayyarta Ghana.

Cristiano Ronaldo na ci gaba da yamutsa hazo a duniyar ƙwallon ƙafa a makon nan sakamkon hirar da ya yi da Talk TV, inda ya zargi ƙungiyarsa ta Manchester United da “yaudarar sa”.

Kazalika, ya ce “ba na girmama koci Eric ten Hag saboda shi ma ba ya mutunta ni”.

Leave a Reply