Tsohon gwamnan jihar Imo Mista Rochas Okorocha, ya bayyana cewa yana kallon haramtattun ‘yan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra a matsayin yaran da suka taso cikin duhun kai da rashin ilimi kwata-kwata amma ba ‘yan ta adda bane.
Mista Okorocha ya bayyana hakan ne ga manaima labarai na fadar shugaban kasa bayan kammala wata ganawar sirri da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kuma ce Wannan yasa ya zargi gwamnatin jihar Imo mai ci da nuna halin ko’in kula kan rikice-rikicen da jihar ke fama dasu masu barazana ga sha’anin tsaro.
Inda yace damuwarsu game da haramta sunanyan kungiyar ‘yan IPOB daga sahun ‘yan ta’adda baza tayi wani tasiri ba.