Robinho zai sha Daurin shekaru 9 a Gidan Yari

An sanar da tsohon dan kwallon Manchester City da Real Madrid, Robinho cewar zai yi zaman yari shekara tara a Brazil kan hukuncin laifin yin fyade.

An samu Robinho mai shekara 40 da laifi a wata kotu a Italiya a 2017, wanda yana cikin taron dangin fyaden da aka yi wa wata mata ‘yar Albania ‘yar shekara 22.

Dan kwallon yana zaune a Brazil, wanda ba a mika shi Italiya ba, to amma alkalai a Brazil sun yanke hukunci ranar Laraba cewar zai yi zaman yari a kasar kamar yadda Italiya ta bukata.

Lauyoyi sun ce yana da lokacin da zai daukaka kara kafin hukuncin ya fara aiki a kansa.

Tsohon dan wasan tawagar Brazil da ya buga wa kasar wasa 100, yana taka leda a AC Milan a lokacin da aka aikata laifin da aka zarge shi.

A shekarar 2020 aka samu dan wasan da laifin aikata fyaden, bayan da ya yi rashin nasarar daukaka kara, inda wata kotu a Italiya ta tabbatar masa da hukuncin.

Daga nan ne masu shigar da kara a Italiya suka mika takardun izinin kamo shi daga Brazil.

Robinho wanda ya yi kaka biyu a Manchester City, ya sanar da wani kamfanin dillacin labarai a Brazil cewar da amincewar matar aka yi lalata da ita.

Dan wasan ya dauki kofin La Liga biyu a kaka hudun da ya yi a Real Madrid daga nan ya koma Etihad a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya kan £32.5m.

An kuma sayi dan kwallon a ranar karshe da za a rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo a Satumbar 2008 – kuma a karon farko da Sheikh Mansour ya fara aiki a matakin wanda ya mallaki Manchester City.

Bayan kaka biyu da City daga nan ya koma AC Milan, kungiyar da ya yi kaka biyar daga nan ya koma China a kungiyar Guangzhou Evergrande.

Bayan da ya kammala taka leda a China, sai ya koma Brazil a kungiyar Atletico Mineiro.

Leave a Reply