Rikicin Zabe: Mutum 6 Za Su Fuskanci Hukunci A Legas

Rundunar ta ce an same su da laifuka daban-daban a Jihar.

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas, ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da mutum shida daga cikin 19 da ake zargi da aikata laifukan zabe a Jihar.

Ana dai zargin mutanen ne da aikata laifukan yayin zaben gwamnoni da na ’yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Rundunar ta kuma ce ta gano dimbin katunan zabe da wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka jefar a wurare daban-daban a jihar.

Rundunar ta ce an jefar da katinan zaben da aka kwato sannan aka yi waje da su domin tserewa.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Benjamin Hundeyin, da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Talata a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), da ke titin Panti, Yaba, ya ce wadanda aka kama suna da hannu a laifuka 21 da suka hada da kai hari kan jami’an INEC da lalata kwace akwatin zabe.

Ya ce za a kuma gurfanar da wadanda don zartar musu da hukunci.

Ya ce hudu daga cikin wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban hukumar zabe ta INEC, yayin da biyu da aka samu da makamai da kuma aikata wasu laifuka za a gurfanar da su a gaban kotu.

Hundeyin ya kara da cewa wasu mutane uku daga cikin wadanda aka kama sun kuma amsa laifin yin garkuwa da su tare da karbar kudin fansa kimanin Naira miliyan 20.7 daga hannun wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply