Rikici ya dabaibaye jam’iyyar NNPP a wasu jihohin arewacin Najeriya
Rikicin cikin gida na ci gaba da turnuƙewa a rassan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP, na wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Hakan na zuwa ne yayin da babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2023 ke ci gaba da matsowa.
Rikicin a yanzu haka ya yi sanadiyyar korar wasu jiga-jigan jam’iyyar yayin da wasu kuma suka sauya sheƙa.

An kori shugaban jam’iyya da ɗan takarar mataimakin gwamna a Sokoto
Rikicin da ya turnuƙe jam’iyyar ta NNPP a Sokoto ya yi sanadin korar wasu jiga-jiganta, ciki har da shugaban jam’iyyar na jiha da kuma mataimakin ɗan takarar gwamna.
Malam Muhammad Abdullahi Bancho dan kwamitin zartarwar jam`iyyar NNPP ne a jihar Sokoto ya ce “gaskiya ne mun kore su saboda mun kama su suna ‘anti-party’”
Ya ƙara da cewa “mun zauna da su kuma sun tabbatar mana lallai sun aikata haka.”
Reshen jihar Sokoto na jam`iyyar ya ce ya daɗe da fahimtar take-taken mataimakin ɗan takaranta na muƙamin gwamna, wato Ibrahim Ango da shugaban jam’iyyar na jiha, Bello Ahmed da wani shugabanta na shiyya.
Kuma jam’iyyar ta ce ta gano cewar suna ƙoƙarin raba kafa ne da wata jam’iyya da nufin ɓata mata tafiya a jihar ta Sokoto.
Ofishin jam’iyyar na ƙasa da ke Abuja ma ya tabbatar da korar jiga-jigan jam’iyyar na jihar Sokoto.
Farfesa Rufa’i Alkali wanda shi ne shugaban jam’iyyar na ƙasa ya shaida wa BBC cewa yanzu haka suna jiran cikakken rahoto ne kan abin da ya faru.
‘Rashin iya tafiyar da jam’iyya ne ya sa muka fita’
Sai dai waɗanda jam’yyar ta ce ta kora a jihar ta Sokoto, ta bakin tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar, Abdullahi Bello Ɗa’a Giɗaɗawa, sun ce fita suka yi da kansu ba korar su aka yi ba.
Jiga-jigan NNPP sun koma APC a Zamfara
Har wa yau a wannan makon ne wasu jiga-jigan jam`iyyar daga ƙananan hukumomi goma da wasu shugabanninta na jiha a jihar Zamfara suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, bisa zargin cewa wasu manyan jam’iyyar na ƙasa suna yin kama-karya wurin tafiyar da harkokin jam’iyyar..
Amma shugabannin NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen su aka yi.
Shugabannin jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmarin sun bayyana cewa da shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar na kananan hukumomi 10 daga cikin kananan hukumomi 14 da ke jihar ne da ƙwansu da kwarkwata suka yi hijira daga NNPP zuwa APC mai mulki sakamakon zargin kama-karya da suka ce ana yi musu.
A cewarsu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu sun yi babakere a jam’iyyar sun hana kowa sakat.
Hon Babangida Haruna Damba shi ne tshon sakataren tsare-tsare na jam’iyyar NNPP a jihar Zamfara da suka jagoranci wannan hijira.
Ya ce “A jihar Zamfara akwai waɗanda suka ci zaɓe amma aka je ‘control room na jam’iyyar na ƙasa inda aka cire waɗannan sunayen mutane waɗanda suka sayi fom suka cika ƙa’ida.
“Daga ƙarshe saboda son rai irin na shi jagora Kwankwaso har jam’iyyar ta rasa ɗan takarar gwamna a Zamfara.”
Ya ƙara da cewa “abin da muka gane shi ne jamiyya ce wadda shi (Rabi’u Musa Kwankwaso) da Buba Galadima sun mayar da ita cewa su ne jam’iyyar.”
Sai dai shugabannin jam’iyyar NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen masu sauya sheƙar aka yi.
Ya ce “mun bayar da sanarwar cewa ciyaman da ɗan takarar mataimakin gwamna sun ajiye muƙamansu da magoya baya.”
Ya ƙara da cewa “mu muka ajiye da kanmu saboda matsaloli da rashin iya siyasa.”
Ba asalin ƴan jam’iyyar NNPP ne suka sauya sheƙa a Zamfara ba – Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima na cikin waɗanda ake zargi da takura shugabannin jam’iyyar, a nasa ɓangaren ya shaida wa BBC cewar jam’iyyar NNPP na da ɗan takarar gwamna a jihar Zamfara.
Ya ce “muna da ɗan takarar gwamnan ANPP a jihar Zamfara, Farfesa Kabiru Jabaka.”
Ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewar shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi goma sun fice, inda ya ce “dama akwai ciyamomin jam’iyya ɗaya ko biyu waɗanda mun san cewa dama gwamnati suke yi ma aiki, su ne suka yi wannan ƙage, Allah raka taki gona, kuma mutanen da aka nuna ba ƴan AMPP ba ne.”